22.5 C
Abuja
Tuesday, August 9, 2022

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga ciyo bashin Naira biliyan 10

Must read

 

A yau Juma’a ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Abdullahi Liman, ta hana gwamnatin jihar Kano rancen bashin Naira biliyan 10 domin kafa na’urar kyamara ta CCTV.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa a ranar 15 ga watan Yuni ne majalisar dokokin Kano ta amince da buƙatar Ganduje ta ciyo bashin Naira biliyan 10 daga bankin Access.

Sai dai kuma wannan ƙudiri ya gamu da tirjiya bayan da Gamayyar Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu, Kano First Forum, KFF, su ka shigar da ƙara mai kwanan wata 27 ga watan Yuni, wanda Darakta Janar na ƙungiyar, Dr Yusuf Isyaka-Rabiu ya shigar.

KFF, ta bakin lauyanta, karkashin jagorancin Badamasi Suleiman-Gandu, ta roki kotun da ta hana Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano ciyo bashin Naira biliyan 10.

Sauran wadanda ake kara a karar sun hada da Babban Lauyan Jihar Kano, Kwamishinan Kudi na Kano da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Sauran sun haɗa da Bankin Access, Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Ofishin Kula da Bashi da Hukumar Kula da Kudi.

Mai shari’a Liman ya amince da roƙon KFF tare da hana wanda ake ƙara na farko cin bashin Naira biliyan 10, sannan ya umarci dukkan ɓangarorin da su dakata da ga ɗaukar wani mataki.

Ya kuma umurci wanda ya shigar da ƙara da ya kaiwa ma’aikatar kuɗi ta tarayya, ofishin kula da basussuka da hukumar kula da kasafin kudi takardar ƙarar da kuma sammaci.

Hukumar KFF na ƙalubalantar Gwamnan Jihar Kano da ya ciyo bashin Naira biliyan 10 bisa dalilan rashin bin ka’idoji da ka’idoji na hada-hadar rance.

Masu ƙarar, a cikin roƙon su, sun kalubalanci gwamnatin jihar ba tare da bin dokar kafa ofishin gudanarwa ta 2003 da dokar kasafin kudi ta 2007 da kuma dokokin jihar Kano na 1968 ba bisa ka’ida ba, inda su ka ce hakan bashi da tushe ba balle makama.

Kotun ta ce za ta sanar da duka ɓangarorin ranar da za a sake sauraron ƙarar.

nnn-news

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article