Home Labarai Kotu a Kaduna ta hana wani mutum shiga dakin tsohuwar matarsa

Kotu a Kaduna ta hana wani mutum shiga dakin tsohuwar matarsa

0
Kotu a Kaduna ta hana wani mutum shiga dakin tsohuwar matarsa

Wata kotun shari’a da ke zaune a Magajin Gari, Kaduna, Jihar Kaduna, ta umarci wani mutum, Aminu Adamu, da kada ya ziyarci dakin tsohuwar matarsa domin ganawa da ‘ya’yansa.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), alkalin kotun, Malam Anas Khalifa, ya yanke hukuncin ne bayan tabbatar da saki uku da Aminu ya yi wa tsohuwar matarsa, Jamila Sani.

“Babu aure a tsakaninku saboda furucin saki da ka yi. Dole ka kaucewa haduwa da ita a sirrance.

“Idan ka na bukatar ganin ‘ya’yanka, ka gan su a wajen dakinta,” in ji shi.

Alkalin ya kuma umarci Aminu da ya ci gaba da daukar nauyin abincin ‘ya’yansa, kudin makaranta, wurin zama da lafiyarsu.

Tun da farko, mai kara, Jamila ta roki kotu da ta tabbatar da furucin saki na uku da Aminu ya yi a watan Yuni kuma ta ba ta ikon riƙe ‘ya’yanta.

Aminu ya kuma yi alkawarin ba tsohuwar matarsa N15,000 duk mako a matsayin kudin ciyarwar ‘ya’yansu.