Home Labarai Kotu ta kori ƙarar Jamhuriyyar kan takunkumin ECOWAS

Kotu ta kori ƙarar Jamhuriyyar kan takunkumin ECOWAS

0
Kotu ta kori ƙarar Jamhuriyyar kan takunkumin ECOWAS

Kotun kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ta kori karar da jamhuriyar Nijar ta shigar gabanta, don tilasta wa shugabannin Ecowas su janye takunkuman da suka kakaba wa kasar, bayan hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum daga mulki a ranar 26 ga watan Yuli.

Shugabannin mulkin soji a Niamey sun ce martanin Ecowas na kakaba wa kasarsu jerin takunkumai ya yi zafi da yawa.

Kuma kungiyar ba ta yi wa kasar adalci ba, idan an kwatanta da sauran kasashen kungiyar kamar Mali da Burkina Faso da Guinea, wadanda su ma suka fuskanci juyin mulki a shekarun baya-bayan nan.

Sun dage a kan cewa takunkuman sun janyo matsin tattalin arziki mai tsanani ga al’ummar Nijar – kasar da ake kallo a matsayin daya daga cikin mafi talauci a duniya.

Kotun Ecowas ta ce ta kori shari’ar Nijar ce saboda shugabannin mulkin sojin da suka shigar da ita, ba su da halasci a bisa doka.

Haka zalika, shugabancinsu ya saba da tsare-tsare da ka’idojin da suka kafa Ecowas.

Takunkuman da Ecowas da sauran kasashe suka kakaba wa Nijar, sun janyo rufe kan iyakoki da dakatar da harkokin kudi da ita, sannan an rufe dukiyar Nijar da ke kasashen waje.

BBC Hausa