Categories
Kanun Labarai

Ba zamu yi dokar da zata hana makiyaya kiwo a yankunanmu ba – Gwamna Simon Lalong

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya bayyana cewar Gwamnatinsa ba zata yarda da wata doka da zata hana Fulani makiyaya kiwo a jiharsa ba. Jihar mu waje ne da ya dace da kiwo domin akwai yanayi mai kyau a jihar Filato wanda makiyaya zasu so yin kiwo a cikinsa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jaridu bayan da ya fito daga fadar Shugaban kasa, bayan ya gama tattaunawa da Shugaba Muhammadu Buhari a Villa dake Abuja.

Lalong yace, tun farko sai da ya baiwa Gwamnan jihar Binuwai Ortom shawara, akan kada ya yarda da duk wata doka da zata hana makiyaya yin kiwo a jiharsa. Domin kuwa wadannan makiyayan ba su da wata hanyar da zasu ciyar da dabbobinsu sama da yawon kiwo.

“A lokacin da Gwamnan jihar Binuwai yake yin wannan doka, na gaya masa cewar, yabi a hankali, ya kamata ya duba dama da hauni kayin aiwatar da wannan doka amman yaki ji”

“Amma sai yace min akwai bambanci tsakanin jiharsa da tawa. Na gaya masa cewar ni ba zan yi wannan doka ba”

Zamu kawo muku cikakkiyar tattaunawar da yayi da ‘yan jaridu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *