Home Labarai Kotu ta wanke ɗan shekara 42 da ake zargi da kisan kai a Kano

Kotu ta wanke ɗan shekara 42 da ake zargi da kisan kai a Kano

0
Kotu ta wanke ɗan shekara 42 da ake zargi da kisan kai a Kano

 

 

 

Wani magidanci, Mustapha Lawan, mai shekaru 42, ya shaƙi iskar ƴan ci bayan da kotu ta wanke shi ta kuma bashi umarni ya koma cikin iyalinsa ya cigaba da rayuwa bayan kisa da ake zargin ya aikata.

Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola na Babbar Kotun Shari’ar Musulunci dake kofar Kudu a Kano shi ne ya jagoranci Shari’ar wacce aka fara tun shekara ta 2021.

Tun da fari dai a na zargin Lawan da kisan wani Umaru, mazaunin Garin Karji, Karamar Hukumar Rogo.

Cikin ƙunshin takardar kara da aka gabatarwa kotun, wacce Lauyan Gwamnati, Barr. A Y Kabara ya gabatar , ta bayyana cewar suna zargin Lawan da shiga gidan marigayi Umaru ya kuma hallaka shi.

Bayan shafe shekara guda ana gabatar da Shari’ar, tare da yin bincike, domin tabbatar da gaskiya, sai dai masu gabatar da ƙara sun gaza kawo shaidun da za su tabbatar da zargin kisan da ake yi wa Lawan.

Mai Shari’a Sarki Yolah a yau Litinin ya gabatar da hukunci, bisa kafa hujjoji daga Malamai da kuma abinda bincike ya gudanar.

Inda Mai Shari’ar ya bayyana cewa iya binciken da su ka gabatar, ya nunar da cewa ba a samu wanda ake zargi da lefin kisan ba.

Haka zalika, Sarki Yolah ya ce daga wannan rana ta Litinin ya sallami wanda ake zargi, kuma ya bada kwanaki 30 ga masu ƙara da su ɗaukaka ƙara idan su na da shakku akan hukuncin.