
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Kano dake zamanta a Abuja, ta sanya ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, 2023 domin fara sauraren karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shigar na kalubalantar soke zabensa da kotun sauraron kararrakin zabe ta Kano ta yi.
A wata sanarwa, kotun ta nuna cewa za a fwra sauraren karar, mai lamba; CA/KN/EP/GOV/KAN/34/2023 a ranar da aka ayyana.
Ɓangarorin da ke cikin karar sun hada da Gwamna Yusuf da jam’iyyarsa ta NNPP, da kuma jam’iyyar adawa ta APC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC.
A tuna cewa a ranar 20 ga watan Satumba, 2023 ne kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta soke zaben Gwamna Yusuf, inda ta bayyana cewa kuri’u 165,663 ba halastattu ba ne domin basu da tambari da sa hannun INEC.
INEC ta bayyana Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga Maris, 2023 bayan ya samu kuri’u 1,019,602 yayin da abokin hamayyarsa Nasiru Gawuna ya samu kuri’u 890,705.
Sai dai bayan da kotun ta cire kuri’u 165,663 daga cikin kuri’u 165,663, an rage kuri’unsa zuwa 853, 939, wadanda suka haura da kuri’u 30,000 kasa da kuri’u 890,705 da Mista Gawuna ya samu.