Home Labarai Kotun koli ta bada umarnin baiwa kananan hukumomi yancinsu na cin gashin-kai

Kotun koli ta bada umarnin baiwa kananan hukumomi yancinsu na cin gashin-kai

0
Kotun koli ta bada umarnin baiwa kananan hukumomi yancinsu na cin gashin-kai

A yau alhamis ne kotun kolin kasar nan ta bayyana cewa daga yanzu duk wani kason da ake baiwa kananan hukumomi ya kamata a biya su kai tsaye a asusunsu.

Mai shari’a Emmanuel Agim, wanda ya jagoranci kwamitin mutane bakwai na alkalan kotun kolin ne ya bayar da umarnin a lokacin da ya ke yanke hukuncin a karar da gwamnatin tarayya ta shigar da gwamnoni jihohi 36.

Yace daga yanzu, ba za a sake biyan kudaden kananan hukumomi zuwa asusun gwamnatin jihohi ba.

Babban Lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) ne ya shigar da karar a madadin gwamnatin tarayya.

Gwamnatin Tarayya ta nemi kotun koli da ta ba da umarni da zai haramta wa gwamnonin jihohi rusa shugabannin kananan hukumomi ba bisa ka’ida ba.