Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jira ga ‘Yan Najeriya da su zabi nagartattun mutane masu amana a yayin da zaben 2019 ke kara kusantowa.

Shugaban yayi wannan kiran ne a yayin da Shugaban Tetfund Baffa Bichi ya wakilce shi a wajen taron Maukibi na darikar kadiriyya da ya gudana a karshen makon da ya wuce.

Haka kuma, Shugaban ya bayyana cewar Gwamnatinsa tayi abin a zo a gani a lokacin da ta yi a mulki, kuma zata sake dorewa idan ‘Yan Najeriya suka zabe ta.