
Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
A gasar Europa kungiyar kwallon qafa ta Arsenal za ta kara da Atletico Madrid ta kasar sipaniya a wasan kusa da na karshe a gasar Europa, yayin da RB Salzburg ta kasar Jamus za ta hadu da Marseille ta Faransa.
Arsenal za ta fara wasan farko ne a gida a ranar Alhamis 26 ga watan Afrilu, sai kuma ta je gidan Atletico a ranar 3 ga watan Mayu mai kamawa
Za a yi wasan karshe na gasar ne a ranar 16 ga watan Mayu a birnin Lyon na kasar Faransa, inda duk kungiyar da ta lashe kofin za ta samu gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai na badi kamar yadda dokar take
Arsenal ta samu nasarar kai wa ga matakin wasan kusa da na karshe ne bayan ta doke CSKA Moscow da jumullar kwallo 6-3 yayinda Atletico Madrid tayi waje da Sporting Lisbon ta Portugal kafin takawo wannan matakin.
Ita kuwa Marseille ta doke RB Leipzig ne ta kasar Jamus a wasansu na baya yayinda Salzburg tayi waje da Lazio ta kasar Italiya a fafatawarsu ta kusa dana kusa dana karshe.