Home Labarai Kullum sai an kashe mutane a Arewacin Nijeriya — Sarkin Musulmi

Kullum sai an kashe mutane a Arewacin Nijeriya — Sarkin Musulmi

0
Kullum sai an kashe mutane a Arewacin Nijeriya — Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmin Nijeriya, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar na 3 ya koka da cewa babu wata rana da ba za a kashe al’umma a Arewacin Nijeriya ba.

Sarkin Musulmin kuma ya shawarci ƴan Nijeriya da su haɗa kansu don kawo karshen ta’addanci a ƙasar.

A lokacin da yake tsokaci kan matsalar tsaro a Nijeriya a taron Majalisar Haɗin kan Addinai, NIREC, Sultan ya ce ba lokaci ba ne da mabiya addinai, musamman Musulmi da Kirista za su riƙa zargin juna da yi wa juna barazana ba.

Sarkin Musulmin ya nuna damuwa kan yadda kashe-kashe da sace-sacen jama’a ke ci gaba da afkuwa, amma kuma Musulmi da Kirista sun ɓige da nuna wa juna yatsa da yi wa juna barazana.

” Dole ne mu daina zargin juna kuma mu haɗa kai matsawar muna son mu yaki makiyanmu. Idan na ce zan yi magana kan rashin tsaro a arewa babu lokacin da za mu bar ɗakin taron nan. In ji Sultan.

Yakara da cewa , “yan kwanakin da suka wuce mun karanta a jaridu yadda aka kona matafiya a bas a Sokoto. Babu ranar da za ta zo ta wuce ba a kashe mutane a Arewa ba, musamman Arewa maso Yamma.”

Bugu-da-ƙari Sultan ya buƙaci shugabanni da sauran hukumomin tsaro su haɗa kai su kuma fahimci girman matsalar tare da magance ta.

“Kar mu yaudari kanmu, abubuwa ba sa tafiya yadda yakamata a Nijeriya. Na sha faɗa a lokuta da dama cewa abubuwa ba sa tafiya yadda ya kamata. Kuma idan dai kasan matsalarka, magance ta ba zai yi maka wahala ba. Saboda haka ya kamata mu san na yi kafin lokaci ya kure mana