Home Labarai AN KUMA: Ƴan bindiga sun kashe sojoji shida a jihar Neja

AN KUMA: Ƴan bindiga sun kashe sojoji shida a jihar Neja

0
AN KUMA: Ƴan bindiga sun kashe sojoji shida a jihar Neja

Rahotanni daga jihar Neja sun baiyana cewa ƴan bindiga sun yi wa sojoji 6 kwanton-bauna a kauyukan Roro, Karaga da Rumace da ke gundumar Bassa a karamar hukumar Shiroro a jihar Neja a daren Juma’a.

An kuma ce an yi garkuwa da wani soja mai muƙamin kaftin a lokacin harin.

Daily Trust ta tattaro cewa sojojin sun bar sansanoninsu ne a Allawa da Erena domin kai ɗauki bayan an yi musu kiran gaggawa cewa ƴan bindiga sun shiga kauyen Roro.

An kuma ce barayin sun kashe wani mafarauci da wasu manoma biyu tare da kona gidaje, bankunan abinci da kuma babura, kamar yadda wasu mazauna garuruwan su ka shaida wa Daily Trust.

Sai dai kuma rundunar sojin ta yi shiru kan lamarin lokacin da wani wakilin jaridar ya tuntube ta a daren jiya Asabar.

Amma kuma Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Neja, Birgediya-Janar Bello Abdullahi Mohammed, a martani ga sakon da wakilin Daily Trust ya aike masa a jiya, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce “mun hada hannu waje guda ” don gano wa da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.