Categories
Labarai

Kungiyar Dattawan Arewa ta nada Farfesa Ango Abdullahi sabon Shugaba

Daga Anas Saminu Ja’en
Kungiyar Dattawan Arewa ta (Northern Elders’ Forum) sun nada Farfesa Ango Abdullahi a matsayin sabon shugaban ta kuma shugaban kwamitin amintattu tare da Alhaji Sani Zangon Daura shi ne a matsayin mataimakin sa inda su ka nemi a gyara harkar tsaro a Najeriya. Kuma an nada wasu kwararru da za su jagoranci ragamar kungiyar ta arewa, irin su Muhammad Bello Kirfi, Yahaya Kwande, Hakeem Baba-Ahmad, Janar Paul Tarfa, Sam Nda Isiah, da sauran su.
Tabbas Farfesa Ango Abdullahi ya cancanta domin kaf fadin arewa a yanzu haka yana daya daga cikin masu nuna kishin arewa tare da damuwa da halin da yanki mutanan arewa ke ciki, Allah ya taya shi riko tare da sauran duk wadanda suka samu mukami, Allah ya kara hada kawunan al’ummar arewacin Najeriya baki daya.
Wannan zabe an yi shi ne a jiya Alhamis tun bayan rasuwar shugaban kungiyar wato Marigayi Dakta Yusuf Maitama Sule Danmasanin Kano, Allah Ta’ala ya gafarta masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *