Alhaji Yusuf Abubakar Dingyadi

Kungiyar matasan ‘yan siyasar Arewa mai suna NOYOPG ta jinjinawa Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar PDP, Sanata Amhed Makarfi, bisa shirya babban taron jam’iyyar da ya zabi sabbin Shugabanni lami lafiya. A lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna, mataimakin Shugaban kungiyar na kasa Yusuf Abubakar Dingyadi, ya bayyana cewar, hakika babban taron jam’iyyar ya zama zakaran gwajin dafi.

“Anyi taro an gama lafiya, kuma wadan da suka ci nasara an san su, kuma ana musu marhabin, amma wadan da sukaci Nasara sune ‘yan Najeriya, da kuma magoya bayan jam’iyyar PDP a duk inda suke a fadin tarayyar Najeriya, da magabatan jam’iyyar, domin anyi taro lafiya an gama lafiya, kamar mai wasa da micijin tsumma, dan kallo lafiya mai wasa lafiya”.

“Dole ne mu yi jinjina ta musamman ga wadan da suka fito takarkaru a mukamai daban daban, da kuma daliget masu zabe da dukkan wadan da suke da ruwa da tsaki, wajen ganin anyi wannan taro lafiya, wannan abin farinciki ne kwarai da gaske”.

“A sabida haka, kafatanin gamayyar kungiyoyin matasan Arewa magoya bayan jam’iyyar PDP suna matukar nuna gamsuwa da wannan babban taro na uwar jam’iyyar PDP ta kasa, musamman nuna sadaukarwa da jajircewa ta kwamitin rikon jam’iyyar karkashin jagorancin Sanata Ahmed Makarfi, bisa sadaukarwar da suka yi ne, abubuwan suka zo da sauki, kuma suka tafi yadda ya dace”.

Alhaji Yusuf Abubakar Dingyadi ya cigaba da cewa, wannan nasara da jam’iyyar ta samu ya biyo bayan, tsayin dakan da tayi wajen ganin ‘yan Najeriya sun samu kyautatuwar rayuwa, da kuma fatan da ‘yan Najeriya suke da shi, na ganin jam’iyyar ta sake samun nasarar darewa kan madafun iko a babban zaben kasa na 2019 dake tafe.

Haka kuma, kungiyar tayi kira ga sabon Shugabancin PDP karkashin jagorancin Uche Secondus da su bude kofar sasantawa da dukkan wadan da suke jin cewar anyi musu ba daidai ba, domin tafiya da kowa tare, a gudu tare kuma a tsira tare.

“Yana da kyau, sabon Shugaban PDP yaja kowa a jiki, musamman masu ruwa da tsaki na jam’iyyar domin baiwa dukkan wanda aka batawa hakuri, domin samun nasarar jam’iyyar anan gaba, sannan kuma, dole shugabancin jam’iyyar ya bayar da damar bai daya ga duk ‘yan jam’iyya ba tare da nuna bambanci ko wariya ga wasu ba”. Inji YusufAbubakar Dingyadi.