
Kungiyar kwadago ta Najeriya,NLC da ta ƴan kasuwa, TUC, sun yi kira ga hukumar kula da samar da wutar lantarki ta kasa NERC da kamfanonin samar da wutar lantarki da su janye karin kudin wutar lantarkin nan da mako guda.
Shugabannin kungiyoyin Joe Ajaero (NLC) daFetus Osifo (AA?, ne suka yi wannan kiran a ranar Larabar da ta gabata a wani jawabi na hadin gwiwa na bikin ranar ma’aikata ta 2024 a Abuja.
Shugabannin biyu sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda ake fama da matsalar farfadiya a kasar da ke shafar ci gaban tattalin arzikin kasar.
A cewarsu, duk wata al’ummar da ba za ta iya sarrafa albarkatun makamashi yadda ya kamata ba, dole ne ta fuskanci lalacewa.
“Daya daga cikin muhimman abubuwan da ke dagula al’ummarmu shi ne gazawarmu a fili wajen gudanar da wannan fanni domin jin dadin rayuwar ‘yan kasa baki daya.
“Wutar lantarki , ko ma daga ina tushen ta ya ke ta kasance mai matukar mahimmanci akan bunƙasa tattalin arziki, yayin da mai da iskar ke zama kashin bayan nasarar samar da makamashi mai inganci a kowace ƙasa,” in ji su.