Marubuci Danladi Haruna

 

Barau Gangariya wani hatsabibin mutum ne da ke iya sarrafa miyagun ƙwari ba tare da sun yi masa komai ba. Yakan ɗauki maciji ya rataya a wuya, ko ya riƙa sa kunama a baki ba ta cije shi ba.
Kowa na shakkarsa saboda hatsabibancinsa amma Malam Idi, wanda ake wa laƙabi  da Ta Faɗa. Shi Idi Ta Faɗa wani irin makwadaicin mutum ne ga yawan roƙo kamar ganyen rogo. A taƙaice dai, ya mayar da rok’o sana’arsa domin kuwa ko yaro k’arami ya gani yana tauna wani abu, ko yana tsotson alewa sai ya fisgi rabonsa daga gare shi. Bayan wannan  dabi’ar tasa ta rok’o sannan Allah ya hore masa tsananin rowa kamar na goye. Idan yana cin abu ya hango wani na tahowa cikin sauri sai ya jefa aljihu ya goge bakinsa kamar dad’ai duniya baya tauna komai.
Duk safiya idan zai fita daga gida ya kan yi karatun  Izawaqa ya shafa ya fita, idan ya samu wani babban mutum ya yi masa maula aka ba shi na goro sai ya kama murna yana cewa, “ta faɗa, ta faɗa” watau Izawaqa ta yi aikin nata.
Rannan ya fito sana’ar maula kamar yadda ya saba, ya zaga ciki da waje, sama da k’asa ya rasa ko sisin kwabo. Dauke batun kudi ma hatta ruwan da zai jika a mak’oshi a ranar nan rasawa ya yi. Ga shi ya yawata har ya gaji. K’ura duk ta bule shi budu – budu kamar wanda aka tono daga kabari.
Da ya gaji da bilumbituwa, sai ya haƙura ya kama hanyar gida domin ya huta. Daga nesa sai ya hangi Barau a kusa da tubani an zuba masa zai soma ci. Mutumin naka sai ya k’ara azama ya zauna gabansa, tun kafin Barau ya kai lomar farko shi ya kai ta uku.
Cikin fushi Barau ya tashi bar masa abincin yana ta zabga loma yana cewa, “ta faɗa, ta faɗa! dai yau bata faɗa da wuri ba.” Bayan ya k’are cinye abinci ya sha ruwa ya yi gyatsa ya kade rigarsa ya yi gaba.
Sai da Barau ya bari Malam Idi Ta Faɗa ya manta da wannan banzar da ya kwasa. Rannan ya dawo daga maula Barau ya hange shi yana tahowa. Ya yi sauri ya ɗauko wani kurtu  yana lakatar wani abu daga ciki yana tandar baki kamar yana shan kayan dad’i. Malam Idi na ganin haka yawun bakinsa ya tsinke, ya ce da shi “Barau me kake sha haka?” Barau ya ce yana tanɗar baki, “Zumumuwa ce kakar zuma.”
“Sammin kad’an mana.” In ji Idi Ta fad’a.
“To bismillah, lakaci kad’an amma fa kar ka shanye min duka na san halinka.”
Idi wanda tuni yawu har zuba yake ya mika hannu zai lakaci zumumuwa. Sa hannunsa ke da wuya cikin kurtu sai kuwa kunama ta gallara masa cizo. Ya cire hannun da sauri yana mai kwalla k’ara. Barau kuwa ya daka tsalle saboda murna yana cewa, “ta fada, ta fada!”
Ashe fisgar hannun da Idi ya yi wata kunama ta makale a hannunsa bai sani ba. Ta sauka akan hancinsa ta sake kwabɗa masa wani cizon. Ya gigice saboda da  azabar zafi. Barau kuwa ya sake daka tsalle yana cewa ta kuma fadawa! Ta kuma fadawa!”
Idi mai kwad’ayi ya tafi gida da kumaburarren hannu da hanci. Bayan ya jima yana jinya ya samu ya warke da kyar. Daga wannan ranar duk sa’adda zai fita bayan karanta izawaqa sai ya yi addu’a ya ce,, “ya Allah ka sa ta faɗa amma kar ta faɗa a irin kurtun Barau.”