Home Labarai Kwamishinan Matasa na jihar Yobe ya rasu a haɗarin mota

Kwamishinan Matasa na jihar Yobe ya rasu a haɗarin mota

0
Kwamishinan Matasa na jihar Yobe ya rasu a haɗarin mota

 

Goni Lawal, Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Yobe ya rasu.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa Tijjani Ciroma, kakakin ma’aikatar ne ya tabbatar da hakan a yau Laraba.

Ya ce Lawal ya rasu ne a wani haɗarin mota da ya rutsa da su a hanyar Potiskum zuwa Azare da misalin karfe 7:30 na yammacin jiya Talata.

Ciroma ya ce marigayin, mai shekaru 57 a duniya yana kan hanyarsa ta zuwa Kano ne domin shiga jirgi zuwa Abuja domin gudanar da aikinsa.

Kakakin ya ce za a yi sallar jana’izar marigayin da misalin karfe 11 na safe a Cibiyar Musulunci ta Yobe da ke Damaturu.

An naɗa Lawal a matsayin Kwamishina a 2019.

Ya kasance mamba na majalisar wakilai daga 2007 zuwa 2015.