A ranar Laraba je ake sa ran Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai kaddamar da takarar neman Shugabancin Najeriya a karkashin tutar jam’Iyyar PDP.

Sanata Kwankwaso na daya daga cikin mutanan da suka sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP a baya bayan nan, kuma yana daga cikin na gaba gaba da suke neman jam’iyyar ta PDP ta basu tikitin tsayawa takarar Shugaban Kasa.

Ko a baya dai, Sanata Kwankwaso yayi takarar Neman tsohuwar jam’iyyarsa ta APC ta bashi tikitin tsayawa takarar Shugaban Kasa, inda ya zo na biyu a zaben fidda gwani, yayin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Nasara.