Home Labarai Lauyoyi 500 sun yi alƙawarin kare Gawuna a Kotun Ƙoli

Lauyoyi 500 sun yi alƙawarin kare Gawuna a Kotun Ƙoli

0
Lauyoyi 500 sun yi alƙawarin kare Gawuna a Kotun Ƙoli

Kimanin lauyoyi masu zaman kansu 500 ne suka yi alƙawarin kare dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar APC, Nasir Gawuna a kotun koli.

Joseph Onwudiwe, mai magana da yawun lauyoyin a karkashin kungiyar masu kula da dimokuradiyya da doka ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja a yau Talata.

Mista Onwudiwe ya ce an yi hakan ne domin inganta dimokuradiyyar kasar.

“Yan Najeriya sun lura sosai da halin da ake ciki a jihar Kano dangane da zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga Maris.

“A matsayinmu na kungiyar da ke da alhakin kare mutuncinmu da dabi’unmu na dimokuradiyya, yanzu ba mu gamsu da hare-haren da ake kaiwa bangaren shari’a ba.

“Kuma wani yunƙuri na bata wa Kotun suna ba. Ba za mu sake naɗe hannayenmu a matsayin lauyoyi ba kuma mu kalli yadda ake ci gaba da cin zarafi da cin mutuncin sashen shari’a ba,” in ji shi.