Home Labarai Layikan waya miliyan 11.2 aka rufe a Nijeriya — NCC

Layikan waya miliyan 11.2 aka rufe a Nijeriya — NCC

0
Layikan waya miliyan 11.2 aka rufe a Nijeriya — NCC

Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, NCC, ta tabbatar da cewa kamfanonin sadarwa sun rufe duk wani layi da ba a haɗa shi da lambar NIN ba.

A makon da ya gabata ne NCC ta bai wa kamfanonin sadarwa izinin rufe layukan kusan miliyan 11.2, wadanda masu su suka kasa haɗa su da lambar NIN.

Umurnin hukumar ya biyo bayan karewar wa’adin watannin da aka baiwa masu wayoyin hannu a shekarar da ta gabata don haɗa layukan su da NIN dinsu kafin ranar 28 ga Fabrairu.

Amma da yake magana a yau Litinin, Kakakin Hukumar, Reuben Mouka, ya ce an kullewa waɗancan masu layukan sakamakon 4ashin maida hankali su haɗa layukan nasu da NIN din su.

Mouka wanda ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a yau Litinin ya bayyana cewa babban makasudin manufar shine inganta tsaro da tsare-tsare na kasa.

“Zai yi wahala a kididdige ainihin adadin layukan wayar da aka rufe. Amma ku ɗauka cewa duk wanda bai haɗa layinsa da NIN ba to am rufe masa shi.

“tun kafin cikar wa’adin ma kamfanonin sadarwa suka fara rufe layuka,” in ji shi.