Home Labarai LGBTQ: Burkina Faso ta yi sabuwar dokar hana auren jinsi

LGBTQ: Burkina Faso ta yi sabuwar dokar hana auren jinsi

0
LGBTQ: Burkina Faso ta yi sabuwar dokar hana auren jinsi

Burkina Faso ta kasance ƙasar Afirka ta baya-bayan nan da ta haramta auren jinsi.

Gwamnatin mulkin sojin ƙasar ce ta sanya hannu kan dokar a lokacin taron majalisar zartaswar ƙasar.

Ministan shari’a na ƙasar Edasso Rodrigue Bayala ya ce sabuwar dokar ta amince ne da auren al’ada da na addini kawai cikin kundinta.

Za a miƙa dokar ga majalisar ƙasar domin saka hannu kafin shugaban mulkin sojin ƙasar, Kaftin Ibrahim Traore ya tabbatar da ita.

A watan Mayun shekarar da ta gabata ne, Uganda ta zama ƙasar Afirka ta baya-bayan nan da ta ɓullo da ɗaya daga cikin dokoki mafiya tsauri kan auren jinsi a duniya.

BBC Hausa