Home Labarai Likitoci sun baiwa gwamnan Legas wa’adin makonni 3 ta ƙaddamar da tsarin albashi na CONMESS

Likitoci sun baiwa gwamnan Legas wa’adin makonni 3 ta ƙaddamar da tsarin albashi na CONMESS

0
Likitoci sun baiwa gwamnan Legas wa’adin makonni 3 ta ƙaddamar da tsarin albashi na CONMESS

Ƙungiyar likitoci sun roki gwamnatin jihar Legas da ta gaggauta aiwatar da shirin ƙarin albashi na tsarin CONMESS na ma’aikatan lafiya, ga likitocin jihar.

Kungiyar Likitocin a karkashin gwamnatin jihar Legas ta ke.

Dr Moruf Abdulsalam, shugaban kungiyar ne ya yi wannan roko yayin wani taron manema labarai a yau Laraba a Legas.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya ruwaito cewa CONMESS shine ma’aunin albashin da ake biyan duk ma’aikatan kiwon lafiya da likitocin hakora a fadin tarayya.

An ƙirƙiro CONMESS ne don hana guduwar likitoci da barin yankunan ƙauyuka.

Abdulsalam ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake tafiyar hawainiya wajen gudanar da aikin karin albashin da aka yi a Legas.

Ya yi nuni da cewa, tuni abokan aikinsu na gwamnatin tarayya suka fara jin dadin biyan albashin tun a watan Fabrairun 2024, tare da wasu basussukan da ake bin su.

Shugaban ya tunatar da cewa kudurin da aka cimma a taron Majalisar da aka gudanar a ranar 27 ga Afrilu, ya yanke shawarar baiwa gwamnatin jihar wa’adin makonni hudu don amincewa da aiwatar da albashin na CONMESS.