
Dakta Maimuna Habib, Babbar Jami’ar kula da Lafiyar Dabbobi ta Najeriya, CVON, ta koka kan karancin kwararrun likitocin dabbobi a ma’aikatar gwamnati a Jihar Plateau.
Habib ta bayyana haka ne a wani shiri na horar da likitocin dabbobi na ISAVET, a yau Talata a Jos.
Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara ta Tarayya ce ta shirya horon, tare da hadin gwiwar Cibiyar ECTAD-FAO.
CVON ɗin ta kuma bayyana cewa a halin yanzu akwai kwararrun likitocin dabbobi huɗu kacal a ma’aikatar noma da raya karkara ta jihar, inda ta ƙara da cewa adadin ya yi ƙaranci.
“A maganar da a ke yanzu, muna da kwararrun likitocin dabbobi guda huɗu kacal a ma’aikatar noma a Plateau; kuma dukkansu suna kan matakim darakta.
“Wannan ba abu bane mai daɗi ga ayyukan likitan dabbobi. Idan jihohi irin su Bauchi suna da likitocin dabbobi sama da 130 da Kebbi 120 a karkashin albashin su, ina ganin Plateau za ta iya yin hakan.
“Don haka, muna kira ga gwamnatin jihar da ta duba wannan al’amari kuma ta yi amfani da karin hannu don tabbatar da lafiyar dabbobi da mutane a cikin jihar,” in ji ta.
Habib ta yi alkawarin tallafa wa gwamnatin jihar wajen inganta harkokin kiwon dabbobi a jihar.