
Akalla ƴan ta’addar Boko Haram uku ne aka kashe a wani harin kwantan-ɓauna da mafarauta da ke aiki da rundunar ‘Operation Hadin Kai’ da ke kusa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa rahotanni sun nuna cewa mafarautan sun damke ’yan ta’addan da ke aikin kwasar ganima a kauyen Wanori da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno a daren ranar Litinin.
Jaridar ta ce, wani mafarauci da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa Zagazola Makama, kwararre a fagen yaki da ta’addanci a tafkin Chadi da faruwar lamarin, inda ya ce mafarautan sun yi wa ƴan ta’addan kwanton ɓauna, inda suka kashe biyu nan take yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Majiyar ta kara da cewa bayan bin ƴan ta’addan da suka raunata ta hanyar da suka tsere, an gano cewa wani mutum guda ya mutu bayan da ya samu raunuka daban-daban.
Majiyar ta ce, “Mun kuma gano wasu guraren 11 da ‘yan ta’addan suka yi amfani da su wajen satar kayan abinci.”