
Wani kare da ake kyautata zaton ya sabu tabuwa, ya ciji mutane uku da dabbobi da dama a kauyen Basaura dake yankin karamar hukumar Jega ta jihar Kebbi.
Daraktan kula da kiwon lafiyar dabbobi na jihar Kebbi, Ahmad Amursa shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a birnin Kebbi ranar Juma’a.
“Wani Kare da ba a san daga ina yake ba kuma ake kyautata zaton cewar tababbe ne ya ciji mutane da dama a kauyen Basaura a karamar hukumar jega”
“karen ya jikkata mutane uku tare da cizon dabbobi da yawa, a sakamakon tabuwa da yayi”