Home Labarai Mai gadi ya rataye kansa a Gombe

Mai gadi ya rataye kansa a Gombe

0
Mai gadi ya rataye kansa a Gombe

Wani mai gadi mai shekaru 38, Abdullahi Ardo, ya kashe kansa a jihar Gombe a ranar Litinin.

Kakakin Rundunar Yansanda a Jihar Bauchi, Mahid Abubakar, ne ya bayyana hakan a jiya a bayanin da ya wallafa a shafinsa na X a jiya Talata.

A cewarsa, marigayin wanda ke aiki a makarantar firamare ta kula da yara, ya yi amfani da igiya ya rataye kansa a sandar lilo.

Ya bukaci mazauna jihar da su rika duba ƴan uwansu domin suna iya fadawa wani yanayi da ke zama barazana ga rayuwarsu.

Ya rubuta, “Don Allah KU GUJI KASAN KAI kuma ku fadakar a kan illar sa. Wani matashi dan shekara 38 mai suna Mallam Abdullahi Ardo da ke aikin gadi a makarantar Child Care Development Primary School, ana zargin ya kashe kansa ne da sanyin safiyar ranar Litinin ta hanyar rataye kansa a cikin makarantar da ke Tudun Wada, Gombe.

“Wannan lamari ne mai ban tausayi; yi ƙoƙari don duba halin da yan’uwanku ke ciki ; za su iya fuskantar manyan matsaloli da ka iya shafar rayuwarsu,” ya kara da cewa.