34.1 C
Abuja
Saturday, April 1, 2023

Mai shafin Northern Hibiscus, Aisha Falke ta karrama manyan ƴan kasuwa a Kano

Must read

 

Wacce ta ƙirƙiri shafin Northern Hibiscus a kafar sadarwa ta Instagram, Hajiya Aisha Falke, ta karrama manyan ƴan kasuwa na jihar Kano.

Taron bada lambar girman, mai taken Mercado Business Icon Ward (MBI), ya gudana ne a jihar Kano a jiya Asabar da daddare.

Da ta ke jawabi a wajen taron, Aisha Falke ta ce ta shirya shi ne domin wayar da kai wajen karfafa gwiwar matasa a harkar kasuwanci domin maida su ƴan kasuwa don a magance matsalar talauci, musamman a arewacin Nijeriya.

A cewar ta, ta shirya taron ne domin karfafa haɗin kai da taimakekeniya tsakanin ƴan kasuwa na jihar Kano da Arewa baki daya domin samun ci gaba mai ɗore wa.

 

Ta kuma ƙara da cewa, taron ya gudana ne domin bayyana wa ƴan kasuwa na Kano shirin ta na samar da Makarantar Koyon Sana’a a Aikace ta Marcedo, domin su bada tasu gudunmawar.

“Idan mu ka samar da wannan makaranta, matasa za su shiga kafin ko bayan sun kammala karatun jami’a. Za su yi watanni 8 kacal kuma su koyi sana’o’i daban-daban.

“Ko da a na yajin aiki a jami’a, ko ɗalibi bai samu gurbin karatu a jami’a da wuri ba, to wannan makarantar za ta taimaka masa ya koyi sana’a kuma ya fara samun kudin kashewa. Hakan zai magance talauci sosai a Arewa,” in jita.

Ta kuma godewa duk wadanda su ka bada gudunmawa wajen tabbatuwar taron.

Daga cikin waɗanda su ka samu lambar girma a taron akwai Alhaji Salisu Sambajo, Alhaji Danlami Alasan, Alhaji Sabi’u Bako, Alhaji Sammani Adamu El-Samad, Alhaji Ahmed Sufaye da sauran su.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article

- Website Designed By DEBORIAN.COM, a Nigerian Web Designer and Web Developer -