Home Ƙasashen waje An sauya wa mata-maza gidan yari bayan da ya yiwa fursunoni 2 ciki a kurkukun mata

An sauya wa mata-maza gidan yari bayan da ya yiwa fursunoni 2 ciki a kurkukun mata

0
An sauya wa mata-maza gidan yari bayan da ya yiwa fursunoni 2 ciki a kurkukun mata

 

 

 

 

An ɗauke wani fursuna mata-maza, Demi Minor zuwa gidan yarin maza bayan ya yi wa wasu fursunoni biyu ciki a gidan yarin mata zalla da ke New Jersey a Amurka.

A cewar jaridar Daily Mail, Minor, wacce ke zaman gidan yari na shekaru 30 bisa laifin kashe tsohon mutumin da ya raine shi a matsayin uba, an dauke ta daga gidan gyaran hali na Edna Mahan zuwa gidan gyaran hali na matasa na jihar a watan Yuni.

Ana tsare da ita a wani waje mafi kazanta a gidan yarin.

Matashiyar mai shekaru 27 da haihuwa, ta koka da yadda masu gadi suka yi mata ba daidai ba da cin zarafi a lokacin canja gidan yarin, har ma an sanya ta a cikin fursunonin da a ke sa musu idanun don kada su kashe kanssu bayan ta yi kokarin ratayale kanta a lokacin da ake kai ta GSCF.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Justice 4 Demi, Minor ta yi ikirarin cewa jami’an gifan yarin na fakon ta, inda daya daga cikinsu ya yi mata ba’a a lokacin da ta a ka ce a tube mata kaya domin bincikar ta.

A wani rubutu na daban, ta yi zargin cewa an yi mata dukan tsiya a lokacin canja gidan yarin.