
Wani ɗan siyasa a Pakistan Hafiz Naeem ur Rehman da ya lashe kujera a zabukan kasar da aka yi kwanan nan ya ajiye muƙaminsa, inda yace an tafka magudi a zaben nasa.
An bayyana Rehman na jam’iyyar Jamaat-e-Islami a matsayin wanda ya lashe kujerar majalisar lardin PS-129 a birnin Karachi bayan ya samu kuri’u sama da dubu 26.
Amma Rehman ya ce ya gano cewa an zabtare kuri’un da aka kada wa dan takarar jam’iyyar Imran Khan na Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI) mai samun goyon bayan jam’iyyar Saif Bari zuwa dubu 11,000 a maimakon dub 31,000 lokacin da aka tattara sakamakon kuri’un da aka kada a rumfunan zabe.
Khan, wanda tsohon firaministan Pakistan ne, yana daure a gidan yari bisa laifin cin hanci da rashawa da kuma laifuka bayan da ya yi da sojojin kasar masu karfin fada-a-ji kuma su ka hana jam’iyar sa ta PTI tsayawa takara, lamarin da ya tilastawa mambobinsa tsayawa a matsayin masu cin gashin kai.
A wani taron manema labarai da jam’iyyarsa ta gudanar a yau Litinin, BBC ta ruwaito Rehman yana cewa: “Idan wani yana son ya sa mu yi nasara ta hanyar maguɗin zaɓe to ba za mu yarda da hakan ba.
“Ya kamata a mutunta ra’ayin jama’a, a baiwa wanda ya yi nasara, wanda ya yi rashin nasara kuma ya hakura, ba wai sai an yi aringizo.”
Ya ce yayin da ya samu kuri’u sama da 26,000, dan takara mai zaman kansa Saif Bari, wanda ke samun goyon bayan PTI, ya samu kuri’u 31,000 – amma sai aka ce kuri’u 11,000 ya samu.
Hukumomin zaben Pakistan sun musanta zargin.
Ba a san wanda zai hau kujerar PS-129 din ba a yanzu.