
Ƴan majalisa 15 a karkashin kungiyar The Economy Rescue Group, sun yi kira shugaban kamfanin mai na kasa(NNPCL), Mele Kyari, da ya yi murabus.
Kungiyar ta yi zargin rashin gudanar da ayyukanta a karkashin jagorancin Kyari a NNPCL ne ya haddasa matsaltsalun da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke ciki.
A wata sanarwa da shugaban ta Hon. Esosa Iyawe, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Oredo a majalisar wakilai a Abuja ya sanyawa hannu a Abuja, ‘yan majalisar sun dage cewa a dakatar da Kyari, har sai an samu sakamakon kwamitin hadin gwiwa na majalisar wakilai kan harkokin man fetur na kasa dake bincike kan halin da kamfanin mai na kasa ke ciki da kuma sassan kasa gaba daya.
Ƴan majalisar dai sun zargi shugaban kamfanin na NNPC da sauran ma’aikatan hukumar da yin zagon kasa ga Ajandar Tinubu ta hanyar cin hanci da rashawa da rashin iya aiki har sai an kammala binciken da majalisar wakilai ta fara ta hanyar kwamitin hadin gwiwa.