Home Labarai Majalisar Dokoki ta Kano na shirin wajabta gwajin lafiya kafin aure

Majalisar Dokoki ta Kano na shirin wajabta gwajin lafiya kafin aure

0
Majalisar Dokoki ta Kano na shirin wajabta gwajin lafiya kafin aure

fiya kafin aure

A jiya Talata ne kudirin da ke son mayar da gwajin cutar HIV, ciwon hanta da sikila kafin aure ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Musa Ali Kachako wakilin mazabar Takai, wanda ya ɗauki nauyin kudirin dokar, ya bayyana a muhawarar sa ta farko cewa jihar ta sha fama da matsalolin lafiya daban-daban da suka haɗa da cutar kanjamau saboda mutane kan yi aure ba tare da an duba lafiyarsu ba.

Ya ce kudirin, idan har ya zama doka, zai ceci rayuka da dama tare da dakile yaduwar cututtuka masu barazana ga rayuwa.

A nashi ɓangaren, Aminu Saad, mamba mai wakiltar mazabar Ungogo, ya ce jihohin Jigawa, Katsina da Kaduna sun zartar da irin wannan kudiri domin magance kalubalen kiwon lafiya da suke fuskanta.

Ya ce tilas ne Kano da ke da mafi yawan al’umma a kasar nan ta zartar da kudirin dokar don kare lafiyar al’umma ta hanyar samar da gwaje-gwajen lafiya kafin aure domin dakile yaduwar cututtuka kamar cutar hanta.

Shugaban majalisar, Ismail Falgore, ya mika kudirin dokar bayan kammala karatu na biyu, ga kwamitin lafiya domin ci gaba da gudanar da ayyukan majalisa tare da gabatar da rahoto ga majalisar nan da makonni 4.