Kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa domin bincike kan bidiyon da jaridar Daily Nigerian ta wallafa kan badakalar da Gwamna Ganduje yake ta karbar kudade a hannun ‘Yan kwangila.

A ranar 14 da 15 ga watan Oktoba ne Daily Nigerian ta wallafa wasu fayafayen bidiyo guda biyu da aka hasko Gwamnan Kano Ganduje yana karbar dalar Amurka daga hannun ‘Yan kwangila yana zubawa a aljihun babbar riga.

Kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa domin bincikar wannan kazamar cuwa cuwa da ake zargin Gwamnan danaikata yasa Kwamitin ya gayyaci mawallafin wannan jaridar Jaafar Jaafar domin bayar da bahasi.

Sai dai bayan da Jaafar Jaafar ya bayyana don bayar da hujjoji gaban kwamitin. Kwamitin ya nemi Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da ya bayyana a gaban kwamitin ranar Juma’a domin bayarvda bahasi kan bidiyon.

Wata majiya ta tseguntawa wannan jaridar cewar, Gwamnan yayi wata ganawa ta gaggawa cikin sirri da kakakin Majalisar dokokin jihar Alhassan Rurum domin ganin bai amsa wannan gayyatar ba.

Sai dai kakakin Majalisar bai gamsu da rokon na Gwamna Ganduje ba na kada a bari ya halarci gayyatar kwamitin. Sai dai Ganduje ba shi da wani zabi a yanzu ko dai ya amsa gayyatar kwamitin ko yasa a tsige kakakin Majalisar abinda zai yi masa matukar wahala.