23.1 C
Abuja
Tuesday, February 7, 2023

Majalisar dokokin Kano za ta binciki dalilin faɗawar Pillars zuwa ƙaramar gasa

Must read

 

 

 

 

Majalisar Dokokin Kano za ta binciki dalilan koma-bayan da Kano Pillars ta samu a Gasar Firimiya ta Ƙasa, NPFL.

Majalisar dokokin jihar Kano ta umurci kwamitin ta mai kula da harkokin wasanni da ya binciki musababbin ficewar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars daga gasar wasannin kwallon kafan firimiya ta Najeriya NPFL.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin, wanda ɗan majalisar dokoki, Alhaji Nurudeen Alhassan, mai wakiltar rano ya gabatar yayin zaman majalisar na yau Litinin.

Cikin kunshin kudirin, Alhassan, wanda kuma shine shugaban kwamitin riko na majalisar, ya bayyana wasanni a matsayin ginshikin ci gaban matasa.

A cewarsa, ficewar Kano Pillars daga gasar wasannin firimiyar wani al’amari ne mai ban damuwa, wanda dole ne a yi bincike matuka don hana afkuwar lamarin nan gaba.

Majalisar ta amince da kudirin baki daya, sannan ta bukaci kwamitin da ke kula da harkokin wasanni da ya gudanar da bincike tare da bayar da rahoto cikin makonni biyu domin ci gaba da aiwatar da dokar.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article

- Website Designed By DEBORIAN.COM, a Nigerian Web Designer and Web Developer -