
Majalisar Wakilai ta bai wa Akanta Janar ta Tarayya, Oluwatoyin Madein wa’adin sa’o’i 72 da ta gabatar da cikakken bayani kan yadda aka yi amfani da kudaden tallafn COVID-19 na Naira biliyan 100 da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta saki ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati tsakanin 2020 zuwa 2022.
Shugaban kwamitin majalisar, mai kula da asusun gwamnati, Bamidele Salam (PDP, Osun), ya ce wa’adin ya biyo bayan gazawar Akanta-Janar din na yin biyayya ga kwamitin na mika rahoton ranar 27 ga Oktoba, 2023.
Ya ce, “An rubuta wasika zuwa ga Akanta Janar domin ta baiwa kwamitin cikakken bayani kan duk wasu bayanai da aka fitar bisa ga tanadin dokar kasafi da kuma sauran tallafi da aka sanya dangane da kuɗaɗen da babban bankin Najeriya ya saki zuwa ma’aikatu da hukumomi daban-daban na gwamnati.
“Wannan wasiƙar, an sanar da ni yadda ya kamata ta nuna cewa ana sa ran gabatar da rahoton a ranar ko kafin ranar 27 ga Oktoba, 2023. Kamar yadda muke magana, ba a sami wannan bayanin daga ofishin Akanta Janar na Tarayya din ba.
“Wannan takarda ce mai matukar muhimmanci da za ta yi mana jagora kan binciken da majalisa ta umarce mu da mu yi cikin wani lokaci”.
Ku tuna cewa majalisar ta, bayan wani kuduri kan kudiri, ta umurci kwamitin da ya binciki “kashe kudaden da aka yi a karkashin ayyukan COVID-19, musamman a cikin 2020 har zuwa 2022.”
Don haka Salam ya umarci AGF da ta mika rahoton kafin rufe aiki a ranar Juma’a 3 ga Nuwamba, 2023