
Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya janye kudurin da majalisar ke shirin tabbatarwa, wanda ya tanadi cewa duk dan Najeriyan da ya kasa rera taken kasar za a ci shi tarar shi Naira miliyan 5, ko kuma ya fuskanci hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari, ko kuma duka biyun.
Abbas ya dai janye kudurin ne bayan cece-kuce da Allah-wadai da aka rika yi wa kudirin a kafafen sadarwa.
Janyewar ta biyo bayan fusata da adawar da ta biyo bayan tanade-tanaden dokar da wasu da dama suka bayyana a matsayin mai tsauri ya kuma saɓawa demokradiyya.
Kudirin da shugaban majalisar Tajudeen Abbas ya dauki nauyinsa, na daga da tsallake karatu na biyu, inda za a yi muhawara kan ka’idojinsa na gaba daya.
A tsarin kudurin, duk wanda ya lalata wata alama ta kasa ko wurin ibada, zai fuskanci hukunci iri daya.
Sai dai bayan bacin rai da adawa da suka biyo bayan kudirin, shugaban majalisar ya sanar da janye shi a yau Laraba.
Sanarwar janyewar ta fito ne daga mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Musa Abdullahi Krishi a yau Laraba.