Home Labarai Ƴan Majalisar Wakilai sun nemi a mayar da shugabancin kasa ya zama shekara 6

Ƴan Majalisar Wakilai sun nemi a mayar da shugabancin kasa ya zama shekara 6

0
Ƴan Majalisar Wakilai sun nemi a mayar da shugabancin kasa ya zama shekara 6

Wasu gungun ƴan majalisar wakilai na neman a sauya kundin tsarin mulkin kasar na 1999 domin share fagen zaben shugaban kasa a tsakanin shiyyoyi shida na kasar nan.

Suna kuma son a yi wa Kundin Tsarin Mulki gyara domin ya tanadi “wa’adi guda na shekaru shida na shugaban kasa da Gwamnonin Tarayyar Najeriya.

Da ya ke jawabi a madadin yan majalisar a yau Litinin a Abuja, mamba mai wakiltar mazabar Ideato South/Ideato North, Jihar Imo, Ikenga Ugochinyere, ya ce, “Raguwar kashe kudade da almubazzaranci da gwamnati ke yi, da nagarta a harkokin mulki, da zaman lafiyar kasa ta hanyar samar da zangon mulki daya na wa’adin shekaru shida na Shugaban kasa da Gwamnoni, zai taimaka matuka wajen rage tsadar kayayyaki.”