Yau da safe aka bayar da labarin rasuwar Malam Inuwa Dutse tsohon kwamishinan gona na farko a Kano zamanin Gwamnatin Marigayi Audu Bako.

Marigayi Malam Inuwa Dutse yayi karatunsa ne a kasar Ingila. Yana da mata hudu da ‘ya ‘ya da yawa, da kuma jikoki masu dumbin yawa.

Malam Inuwa Dutse tun lokacin da ya bar harkokin Gwamnati ya mayar da hankali akan aikin gona, tsaron rayuwarsa koda yaushe yana gona. Yana da katafariyar gona a Kafin Hausa da kuma garin Tiga a Kano.