Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai

Malaman Makarantar Sakandire da na Firamaren Gwamnati a jihar Kaduna a ranar Litinin sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani duk kuwa da barazanar da Gwamnatin jihar ta yi na korar duk wanda ya ya shiga yajin aikin da kungiyar malaman makaranta ta NUT ta kira a dukkan fadin jihar.

A wasu daga cikin Makarantun Gwamnati a cikin garin Kaduna, masu gadi ne kadai ake iya gani a harabar shiga makarantun, a yayin da Malamai da Dalibai babu wanda ya zo Makaranta.

A LGEA Fairamare dake Mahuta da Unguwar Boro masu gadi kadai ake iya gani a harabar kofar shiga makarantun, a yayin da ajujuwa da ofisoshi suke garkame da mukullai.

Daya daga cikin masu gadin yace, babu wani Malami da ya dawo bakin aiki, yace amma wasu dalibai sun zo makaranat inda daga bisani duk suka koma gidajensu sabida babu Malamai.

A makarantar Gwamnati dake Unguwar Muazu, wasu malaman sun je Makaranta amma dai babu dalibai ko kadan da suka zo makaranta dan haka Malaman suka san inda dare yayi musu.

Wani Malamai dai ya roki kada a bayyana sunansa, yace, su ne suka umarci dukkan dalibai da su koma gida sabida sun tafi yajin aiki, ya kara da cewar, wasu Malaman sun dan yi fakare a makarantun ko zasu ji wata sabuwar sanarwa daga NUT.

A Rimi Kwalej dake Unguwar Rimi, wasu malamai da kuma daliban sun zo makaranta, daga bisani kuma jami’an NUT suka zo suna yi musu bayanin tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani, inda nan take malaman suka karbi wannan albishir na tafiya yajin aiki.

Haka kuma, A makarantar Sakandiren Gwamnati dake Unguwar Muazu da kuma maarantar ‘yan mata dake kan titin ‘yanci a Kaduna, Malaman sun bayyana cewar basu sami wata sanarwa daga NUT ba kan batun tsunduma yajin aikin ba.

Wasu daga cikin makarantun da muka ziyarta sun hada da Makarantar Gwamnati dake Tudunwada kan titin Kargi da Firamare dake kan titin Faki duk babu wani abu da yake nuna an koma Makaranta.

Haka kuma, Rahotanni daga Zaria, Sabongari, Makarfi, Soba, Giwa da kuma karamar hukumar Ikara na nuna duk sun tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gai da NUT ta kira a dukkan fadin jihar.

Shugaban NUT na karamar hukumar Zaria, Malam Yahaya Abbas yace, Yajin aikin ita ce kadai hanyar da Gwamnati zata iya sauraron Malamai, domin dukkan wani yunkuri da aka yi a baya bai ci nasara ba, dan haka babu wani abun da ya rage face tsunduma wannan yajin aiki.

Zamu cigaba da Kawo muku bayanai kan wannan yajin aiki.