Home Nishaɗi Manhajar kallon fina-finai ta yanar gizo, kallo.ng ta samu lambar girma a Ghana

Manhajar kallon fina-finai ta yanar gizo, kallo.ng ta samu lambar girma a Ghana

0
Manhajar kallon fina-finai ta yanar gizo, kallo.ng ta samu lambar girma a Ghana

 

Watanni takwas kacal da ƙaddamar da manhajar kallon fina-finan Hausa ta yanar gizo, mai suna kallo.ng, ta samu lambar girma a Ghana.

Kallo.ng ta samu lambar girman ne daga Marketing World Award, MWA, kamfanin da yayi shura wajen bada lambar girma ga wadanda su ka yi bajinta a harkar finafinai.

An bada lambar girman ne a ranar 15 ga watan Yuli, a wani katafaren taro da s ka yi a birnin Accra na ƙasar Ghana.

A wata sanarwa da ta fitar a Kano a jiya Asabar, shugabar kallo.ng, Hajiya Maijidda Moddibo, ta bayyana cewa lambar girman wata gagarumar nasara ce.

A cewar ta, kamfanin ma kallo.ng ya samu nasarar ne duba da irin jajircewarsa wajen ganin ya inganta manhajar, wajen amfani da sabbin fasahohin zamani, don biyan buƙatar abokan hulɗarsa.

Maijidda ta kuma ƙara da cewa kamfanin kallo.ng ya tsaya kai da fata don ganin ya mayar da manhajar ta zama daidai da tsarin tafiyar da manhajar kallon fina-finai na duniya.

Ta kuma bayyana cewa yanzu haka kamfanin na kallo.ng, duba da irin dabarun zamani da ya ke bullowa da su, ya samu sama da mutane dubu 35 da su ka kulla alaƙa da shi.

Ta kuma ci alwashin ci gaba da inganta ayyukan kamfanin don biyan buƙatar abokan hulɗa.