Home Labarai Manyan jami’an mu uku sun mutu a mako biyu– Rundunar ƴan sandan jigawa

Manyan jami’an mu uku sun mutu a mako biyu– Rundunar ƴan sandan jigawa

0
Manyan jami’an mu uku sun mutu a mako biyu– Rundunar ƴan sandan jigawa

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta ce manyan jami’anta uku sun mutu sakamakon rashin lafiya a cikin makonni biyu da suka gabata.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Lawan Shiisu ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a yau Litinin a Dutse, babban birnin jihar.

Shiisu ya ce jami’an sun mutu ne tsakanin 22 ga watan Yuni zuwa 5 ga watan Yulin wannan shekarar.

A cewarsa, wadanda suka mutu sun hada da SP Salisu Salisu-Mudi, wanda ya rasu a cibiyar lafiya ta tarayya dake Katsina a ranar 22 ga watan Yuni.

Sauran, sun hada da ASP Asabe Muhammad, shugaba ta biyu a sashen binciken manyan laifuka na jihar, wadda ta rasu a ranar Laraba, sai DPO na sashen Yankwaahi, CSP Muhammad Salihu-Koko, wanda ya rasu ranar Juma’a.

Ya ce rundunar ta jajantawa iyalai da ‘yan uwan mamatan, yayin da suke addu’ar Allah ya jikan su.