Home Labarai Martani game da cire ni daga sarautar Mujaddadin Bauchi — Sanata Shehu Buba

Martani game da cire ni daga sarautar Mujaddadin Bauchi — Sanata Shehu Buba

0
Martani game da cire ni daga sarautar  Mujaddadin Bauchi — Sanata Shehu Buba

Na samu labari Mai cike da ban mamaki game da wasika Mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Augusta inda ake sanar dani cewa Majalisar masarautar Bauchi ta cire ni daga mukamin sarautar mujaddadin Bauchi sakamakon zargin cewa na ci mutunci ko zagin Gwamnan jihar Bauchi a wani gangamin yakin neman zabe.

Ina amfani da wannan dama in sanar da cewa tun sanda na shiga siyasa bana bin wani tsari face suka mai Maana,ba tare da cin mutunci ko zagi ba ,Kuma tsarin da nake bi tsari ne na nufin samar da ingantacciyar Al’umma.

Lokacin da na saurari kalaman Gwamna Bala Muhammad akan Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu sai naga hakan ya kasance wajibi gare ni da na Kare Shugaban kasar daga yunkurin da ake yi na batawa da lalata Kimar sa da saka kiyayyar sa a zukatan Al’umma,Wanda haka nayi a yakin neman zaben da APC tayi da na halatta kwanannan .

Amma Kuma maganganun Gwamna Bala Muhammad akan Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu wanda kafafen yada labaran kasar nan da dama suka rawaito sun hada da fito na fito ,da zargi mara tushe da kuma kage, da amfani da kalamai da ka iya kawo barazana ta tsaro a kasa a maimakon dalilai na hankali.

Kuma Ina so In jadda da cewa zarge zargen da Gwamna Bala Muhammad yayi wa Shugaba Tinubu, kalamai ne na siyasa, basu da tushe ,haka Kuma basu da wata cikakkiyar hujja da dalilai.

Sannan a kalaman da nayi na musanta zargin da Gwamna Bala ya yiwa Gwamnatin Tinubu na rashin Kula da aiki da Kare hakkunan al’ummar kasa amma na zargi Gwamna Bala da aikata hakan.

Sannan a jawabin da nayi nace Gwamna Bala Muhammad ya karbi Naira Biliyan 144 daga asusun Gwamnatin Tarayya a Shekarar 2023 da Kuma fiye da Naira Biliyan 47 daga watan Janairu zuwa yau Wanda ake sa ran a jumlace zasu kai Naira Biliyan 195 zuwa karshen wannan shekarar .inda na nemi bahasi akan cewa me Gwamnatin Bala Muhammad tayi da wadannan kudade.

Saboda haka na Kara da cewa zargin da Gwamna Bala ya yiwa Shugaba Tinubu basu da tushe ballantana makama Kuma kalamai ne na siyasa.

Sannan a jawabina na tuhumi Gwamna Bala Muhammad da ya Fadi abunda yayi da makudan kudade Dake asusun Jihar ta Bauchi sakamakon yadda Al’umma ke kukan yunwa duk da cewa Gwamnatin ta karbi biliyoyin Naira daga asusun Gwmantin Tarayya.

Sannan nace Shugaba Bola Ahmad Tinubu na yin iya kokarin sa na Samar da tsaro a Fadin Tarayyar Najeriya ,da daidaita Tattalin Arziki da Kuma ganin an samu zaman lafiya tsakanin Yan kasa ba tare da rabuwar Kai ba Wanda Shi Gwmana Bala ba haka yake ba.

Kalamai na nayi su ne da kyayyakwar niyya da Kuma Kare shugabanci na sama ba na matakin Jiha ba.sannan ina mamaki da nadamar yadda Majalisar masarautar Bauchi ta gaggauta Yanke hukunci akan kalamai na ba tare da taji ta bakina ba,saboda haka matsayar da Majalisar masarautar ta Bauchi ta yanke akai na na karba da kyakkyawar niyya ,sannan ina da saka rai cewa Allah madaukakin sarki zai aiko da wani maceci da zai zo ya ceci jihar Bauchi daga halin da take ciki.

Sannan Ina shawartar Majalisar masarautar Bauchi da ta guji amfani da wasu ka iya yi da ita domin cimma manufofin su na san Rai da Kare muradun wasu .Sannan ina Addua Allah ya ja zamanin mai martaba Sarkin Bauchi da lafiya domin tafiyar da wannan masarauta.

A wannan jawabi nawa na hada da Kwafin zargin da Gwamna ya yiwa Shugaba Tinubu a shirye shirye da akayi da shi kai tsaye tare da Kuma martani da na mayar.

Ina Godiya matuka Kuma Ina Mika jinjina da Gaisuwa

Sa hannun

Sanata Shehu Buba Umar

Shugaban Kwamitun Majalisar Dattijai na tsaro da tattara bayanai.