Sheikh Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo

Fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan da ke jihar Kano Sheikh Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya mayar da martani akan masu sukar Saudiyya akan shirin ta na samar da cibiyar Hadisi a birnin Madina mai tsarki. A yayin da yake zantawa da wakilinmu, Dr. Sani ya bayyana cewar muguwar fassara ce ace biyewa Amurka ne samar da wannan cibiya.

A cewarsa, samar da wannan cibiya, ya biyo bayan kiraye kirayen da Malamai a kasar suka yi ne domin samar da wannan cibiyar. Ya kara da cewar, akwai cibiya ta Alqurani wadda kasar ta samar zamanin Sarki Fahad, wadda ake buga tare da fassara alqurani zuwa harsuna daban daban a duniya.

Ya kuma kara da cewar, samar da wannan cibiya zata taimaka wajen yiwa addini hidima, domin fassara da kuma yada litattafan hadisi. Yin hakan zai sa a tsare litattafan hadisi daga gurbatacciyar fassarar da gurbatattaun Malamai suke yi ga Hadisan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam.

Haka kuma, Malamin ya nesanta kasar ta Saudiyya da cewar tana horar da Malamai ‘yan ta’adda. Yace sun kwashe shekaru masu tsawo suna karatu a kasar amma gasu duk cikin su babu wanda yake da alaka da ‘yan ta’adda balle ace suna koyo ta’addanci a kasar ta Saudiyya.

Da yake bayani kan masu tsattsauran ra’ayi, Malamin yace tsabar jahilci ne yake damun su, domin suna fassara alqurani ne bisa jahilci ba tare da sunyi la’akari da fahimtar magabatan wannan al’umma ba. Ya karaa da cewar,kokarin raba Musulmi ne da Saudiyya shi yasa ake jinginawa kasar ta’addanci.