Daga Hassan Y.A. Malik

Wasu mazauna jihar Legas da ke son tafiya garuruwansu don gabatar da bikin Ista (Easter) da ma mutane ‘yan gari da ke amfani da titina sun nuna rashin jin dadinsu da yadda ziyarar aiki na kwanaki 2 (daga Alhamis zuwa gobe Juma’a) da Shugaba Buhari ya kai ya haddasa musu wahala na babu gaira babu dalili sakamakon wasu titinan jihar da gwamnati ta yi.

Wasu matafiya da za su bi jirgin sama sun nuna takaicinsu kan yadda suka yi tafiyar kafa mai nisa zuwa tashar sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas din.

Tun da misalin karfe 5:00 na asubahin yau ne dai jami’an tsaro suka fara shingace titinan Agege Motor Road, Airport Road da titin Mobolaji Bank-Anthony da sauran kananan titinan da suka hada wadannan titina.

Shugaba Buhari zai shigo jihar Legas ne don ya kaddamar da wata babbar tashar mota ta zamani da gwamna Ambode ya gina, wacce aka yi wa suna da Ikeja Bus Terminus da dai sauran sauran ayyukan gwamnan Legas din da ya ke so Buhari ya kaddamar.

Wannan ziyara ta shugaban kasa, da matakin tsaro da rage cinkoson ababen hawa da gwamantin jihar Legas ta dauka ya shafi lokutan tashin jiragen sama, inda da dama suka kara sama da awa guda don su jira fasijojin da ko dai cinkoso ya tare su, ko kuma wadanda aka sauke a nesa da tashar jirgin kuma suka taka zuwa filin jirgin.

Kamfanin Air Peace ala dole ya soke tashinsa daga Legas zuwa Jos na safiyar yau. Shi ma kamfanin Arik Air an ji yana ta bawa fasinjojinsa na Legas zuwa Fatakwal na karfe na safe hakuri da su dan saurara kadan don jiran wadanda halin da ake ciki ya hana karasowa akan lokaci.

Sai dai kuma, Darakta mai lura da harkokin jama’a na hukumar filayen jiragen sama na kasa, Mrs. Henrietta Yakubu ta bayyana cewa ta bayyana cewa rufe hanyoyin da kuma hana motoci shiga da fita daga filin jirgin saman Murtala Muhammed da gwamnati ta yi, ta yi hakan ne don Shugaba Muhammadu Buhari ya samu wucewa a hanyoyin Legas cikin sauki.

Wani kwararre akan harkokin sufurin jirgin sama kuma mai fada a ji a harkae sufurin jirgin sama na kasa, Kyaftin John Ojikutu mai ritaya, ya bayyana rufe titinan da za su kai fasinjojin jiragen sama zuwa filin jirgi a matsayin wani shiri da ya kawo wa matafiya rashin jin dadi.

“Bai kamata a ce zuwan shugaban kasa ya saka a jefa mutane cikin wani hali ba. Kamata ya yi a ce a bar ababen hawa su kawo fasinjoji har zuwa gidan mai na Forte Oil, kusa da shataletalen caji ofis na Bisam.

Wasu matafiya biyu, Mista Ejike Agu da Mista Augustine Iweh sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN cewa kamata ya yi a ce a aikewa da matafiya sako na musamman kan batun rufe hanyoyin da za su kai su filin jirgi don su shirin kar ta kwana.

Mista Agu ya ci gaba da cewa wasu daga cikinmu za su yi tafiya ne zuwa garuwansu don yin hutun Ista, sam bai kyautu ba abinda aka yi mana ba na rufe hanyoyin da za su kawo mu tashar jirgi. An saka min yi tafiyar kafa daga wuri mai nisa zuwa inda za mu hau jirgi.

Shi kuma Iweh cewa ya yi, ya yi sa’ar samun direban tasi da ya san gari, inda ya yi ta kurdawa da shi lunguna da sakuna har ya kawo shi tashir jirgin, amma ya caje shi Naira 5,000.