Daga Abdulrazak Ibrahim

Shehunnan malaman kimiyya a ƙasar Amurka da suka haɗa da Jeffrey Hall na jami’ar Maine da Michael Rosbash na jami’ar Brandeis da Michael Young na jami’ar Rockefeller sun lashe kyautar lambar yabo ta Nobel ta kimiyyar likitanci ta bana.

A bayanin kyautar da aka sanar da ita a Nobel Assembly dake Karolinska Institute a ƙasar Sweden a yau Litinin 2 ga Oktoba, ta bayyana cewa an basu lambar yabon ne “…domin bincikensu ya gano yadda tsirrai da dabbobi da bil Adama kan sarrafa ƙwayoyin halittunsu ya daidaita da kewayen da duniya ke yiwa rana”.

Shi dai wannan yanayin bincike da ake kira Circardian rhythm ko kuma ace agogon likimo, yana nuna yadda yanayin cikin halitta kan canja sakamakon canjin lokaci musamman zafi da hasken rana.

Wadannan canje-canje sun shafi bacci da canjin zafin jiki (body temperature), walwalin kwakwalwa (brainwave) da ɗabi’a da gina sabbabin ƙwayoyin halitta da sauransu.

Binciken nasu ya gano ƙwayoyin halittun DNA (wato genes) ɗin da ke da alhakin karbar sako daga hasken rana, ya turawa ƙwakwalwa ita kuma ta aika da saƙon cikin jiki don jiki ya yi barci, ko ya huta ko kuma ya wartsake da dai sauransu.

Lambar yabon da waɗannan masu bincike suka samu ta haɗa da kyautar maƙudan kuɗi miliyan 9 na ƙasar Sweden, kimanin miliyan 400 ta naira.