Mazauna garin Ijemo da ke unguwar Oba Ademola a garin Abeokuta a jihar Ogun, sun bayyana damuwarsu kan yadda barayi ke ci gaba da mamaye al’umma.
Jaridar PUNCH Metro ta tattaro cewa a daren Juma’a ne ɓarayin su ka shiga wasu shaguna a yankin, inda suka yi awon gaba da wasu kayayyaki masu daraja.
Wasu daga cikin mutanen da lamarin ya rutsa da su da kuma mazauna wurin da suka zanta da manema labarai sun yi kukan cewa barayin sun lalata makullan kofofin shaguna da dama a yankin.
Mazauna yankin sun koka kan yadda al’umma ke fuskantar hare-hare daga barayin da har yanzu ba a kai ga gano su ba.