
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi zargin cewa batagari sun sace takardun tuhume-tuhumen da ake wa tsohon Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da iyalansa a yayin zanga-zangar matsin da ta gudana a farkon watan nan.
Ganduje, wanda shine shugaban jam’iyyar APC na kasa, yana fuskantar tuhume-tuhume kan zargin cin hanci da rashawa a gaban babbar kotun jihar.
Sai dai kuma a ranar farko ta zanga-zangar, sai wasu ɓatagari su ka kutsa kai cikin ginin Babbar Kotun Jihar, inda su ka yi fashe-fashe da kone-kone da sace-sace, inda a nan ne su ka sace takardun shari’ar Ganduje, in ji Gwamna Yusuf.
Zargin na dauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a yau Laraba.
A cewar sanarwar, Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar duba irin barnar da aka yi a babbar kotun.
“Abu ne na takaici cewa makiya jihar Kano sun yo hayar ƴan daba don lalata daya daga cikin gine ginen tarihi bisa burinsu na lalata tuhumar da ake yiwa shugaban APC na riko na kasa da iyalansa da hadimansa”, inji shi.
Gwamnan, wanda ya bukaci matasa su kaucewa shiga duk wani nau’i na tarzoma ya sha alwashin gyara ofisoshin da aka lalata a yayin zanga zangar.
Ya kuma baiyana cewa barnar da aka yi a ginin ta haura Naira biliyan daya.