A kalla mata 30 ne suka haihu a sansanin ‘yan gudun hijira dake Gandi a jihar Sakkwato, su dai wadannan ‘yan gudun hijira sun fito ne daga kauyen Tabanni dake yankin karamar hukumar Rabah a jihar ta Sakkwato.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Sakkwato Alhaji Ibrahim DIngyadi shi ne ya bayyana hakan ga mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Saad Abubakar na uku a lokacin da ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijirar.

“A kalla akwai ‘yan gudun hijira 4,996 da suka fito daga kusan kauyuka tara na jihar Sakkwato bayan da ‘yan ta’adda suka farma garuruwansu da hare haren ta’addanci”

Dingyadi ya bayyana kauyukan da ‘yan gudun hijirar suka fito kamar haka: Tabanni da Gidan-Kare da Kursa da Warwasa da Rumbun-Tsamiya da Tudun-Kwasa da Dutsu da Illilu da kuma ‘Yankusar-kilawa.