
Wata ƴar kasuwa, Monica Gambo, a yau Juma’a ta maka mijinta, Yakubu Gambo a gaban wata kotun gargajiya da ke Nyanya Abuja, saboda ya hana ta haƙƙoƙinta na aure.
Mai shigar da ƙarar, wacce ke zaune a Nyanya, ta faɗi haka ne a cikin takardar ƙorafi da ta shigar a gaban kotu.
“Mijina mazinaci ne, sai ya riƙa kawo yan matansa gida na ya na zina da su.
“Ni kuma ya hana ni duk wasu haƙƙoƙi na na aure, sabo da haka ni ba zan iya ci gaba da zama da shi ba,” in ji ta.
Ta kuma shaida wa kotun cewa mijin nata ya sha yi mata barazanar kashe ta tare da ƙwace mata dukiyata.
Sabo da haka ta ke rokon kotu da ta raba aurenta tare da ba mijinta umarnin ya bar mata gidanta.
Wanda ake kara, Yakubu Gambo, wanda ke sana’ar ɗinki, yana gaban kotun kuma ya musanta zargin.
Alkalin kotun, Shitta Mohammed, ya ɗage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 20 ga watan Satumba.