
Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu ya ce shiri ya yi nisa na koyawa matasan arewa maso yamma su dubu fasahar zamani ta AI.
Kalu ya baiyana haka ne a wajen taron yaye matasa 2,000 da Better Life for Children and Women Future Foundation ta yi a juya Lahadi a jihar Kano.
Ya ce ya ɗauki gaɓaran horas da matasan ne domin bada gudunmawar da wajen cigaban matasa a Arewa da Nijeriya baki daya.
Kalu, wanda ya samu wakilicin Mataimakin sa na musamman, Tayyib Saleh Danpullo, ya kuma baiwa ƙungiyar tallafin naira miliyan 30 domin baiwa matsana da aka yaye harin sana’o’in da suka koya daban-daban.
Ya ce matasa sune kashin bayan cigaban ko wacce al’umma, dan haka ya dage wajen tallafa musu.
Kalu, wanda dan yankin Kudu maso Gabas, ne amma ya zo Arewa ya ke taimakawa matasa, yace zai ci gaba da irin wannan hobbasar ta taimakawa matasa.