Crystal Harris na sumbatar marigayi Hugh Hefner

Daga Mustapha Usman

Mashahurin tsohon nan Hugh Hefner wanda ya yi shuhura wajen yaɗa batsa bai barwa matar da za ta yi masa takaba ko taro ba.

Hefner ya mutu ranar Talata bayan shafe shekaru 91 a duniya, kuma da shafe fiye da shekaru 50 yana fasadi a doron kasa.

Duk da cewa sun yi zaman aure na kimanin shekaru biyar da matar tasa mai suna Crystal Harris kafin mutuwarsa, sai dai a cikin wasiyyar da ya bari ya ce kada a bata ko taro cikin makudan kudin da ya bari.

An ƙiyasta dukiyar da ya bari kimanin dalar Amurka miliyan 110 ce, sai dai wata majiyar kuma ta ce bai kai hakan ba.

A cikin wasiyyar da ya bari, dukiyar tasa za’a raba ta ne tsakanin ‘yayansa hudu da ya bari da Jami’ar Kudancin California da kuma fannin taimakawa mabuƙata. Ita kuwa Crystal ya ce kawai a kula da dawainiyarta.

Sai dai rahotanni sun yi nuni da cewa kafar walan da Hefner ya yi Crystal ramuwar gayya ce saboda wahalar da ta bashi kafin a yi auren.

Me nene ra’ayinku a kan wannan ƙafar wala da ya yi mata?