
Matasa a jihar Kano, ƙarƙashin ƙungiyar ‘One Voice Development Initiative’ sun yi addu’a ta musamman kan domin neman Allah Ya sa a saki da sandan nan DCP Abba Kyari.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Kyari, dan sandan da ya yi suna wajen kama masu garkuwa da mutane, na nan a ɗaure a gidan yarin Kuje bisa tuhume-tuhumen laifuka daban-daban.
Da ya ke jawabi yayin gudanar da addu’ar, shugababn ƙungiyar, Abbas Yakasai ya ce sun dukufa wajen yin addu’ar fitowar Kyari ne domin muhimmancin sa a harkar tsawon Nijeriya.
A cewar Yakasai, kungiyar na da yakinin cewa Kyari mutum ne mai rikon amana da aiki tukuru, inda ya kara da cewa *Nijeriya ta fi samun zaman lafiya lokacin da Kyari ke aiki kafin a kama shi.”
*Shi ya sa muke kira ga mahukunta su sake shi domin mu a ganin mu bashi da wani tabbataccen laifi da ya yi.
“ A sake shi ya dawo aiki domin Nijeriya na bukatar shi a halin yanzu,x in ji Yakasai.
Yakasai ya kuma roki shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ya sa hannu domin a saki Kyari.